Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Aminu Ado Tarar N10m

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Kano ta zartar da hukunci a kan taka hakki tare da muzgunawa tsohon sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta hanyar fitar da shi daga fadar masarautar Kano ba tare da shiri ba.

A hukuncin da kotun ta zartar, ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta biya Aminu Ado tarar kudin da yawansu ya kai miliyan goma cikin sa’a 48, wato kwana biyu.

A watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Aminu Ado daga kan kujerar sarkin Kano tare da bashi umarnin ya mika mulki cikin sa’a 48.

Duk da ba ya cikin jihar Kano a lokacin da aka bayar da umarnin tube shi, Aminu Ado ya dawo Kano tare da komawa karamar fadar sarki da ke unguwar Nasarawa wanda rashin jin dadin haka ya sa Abba ya bayar da umarnin a kama shi.

Sai dai, Aminu Ado ya garzaya kotu domin kalubalantar umarnin Abba tare da neman alkali ya warware tube shi da mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar sarkin Kano.

Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni, alkalin kotun, Simon Amobeda, ya bayyana cewa kotunsa na da hurumi tare da ikon yanke hukunci a kan duk wani korafi na taka hakki.

KARANTA: Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

Mai shari’a Simon ya bayyana Aminu Ado yana da iko da damar zuwa ko zama a ko ina yake so a cikin Kano ko kuma cikin Najeriya.

Sai dai, kotun ta ki bayar da umarnin cewa Sarki Sanusi ya fice daga fadar masarautar Kano.

Lauyan sarki Sanusi II da gwamnatin jihar Kano, Ibrahim Isa Wangida, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara ga Aminu Ado da magoya bayansa duk hakan bai shafi halacci ko haramcin dokar da ta dawo da sarki Sanusi II ba,

Ya kara da cewa zai tuntubi wadanda ya ke wakilta kafin ya iya cewa wani abu a kan ko zasu biya tarar N10m ko kuma su daukaka kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories