Gwamnati Ta Nada Ba-Amurke A Matsayin Dillalin Siyar Da Jiragen Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga manya da kananan kafafen yada labarai a Najeriya sun rawaito cewa gwamnatin tarayya ta saka uku daga cikiin jiragen fadar shugaban kasa a kasuwa domin a siyar da su a siyo sabbi guda biyu.

A wani rahoto da jaridar The Cable ta wallafa, ta bayyana wani kamfanin harkokin jirage na kasar Amurka mai suna ‘JetHQ’ shine wanda gwamnati ta nada a matsayin dillalin jiragen da za a siyar.

Jiragen fadar shugaban kasa da za a siyar sune Boeing 737, BBJ; wanda shine aka kebe domin amfanin shugaban kasa, Gulfstream, da kuma Falcon 7x.

Akwai jirage guda shida a ayarin jiragen fadar shugaban kasa da suka hada da uku masu saukar Ungulu.

Sai dai, kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin tsaro ya ce dukkan jiragen sun tsufa kuma suna dauke da matsaloli daban-daban da bai kamata shugabann kasa ya cigaba da amfani da su a haka ba domin kiyaye rayuwarsa da lafiyarsa.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana wa manema labarai cewa za a siyar da uku daga cikin jiragen ne domin a yi amfani da kudinsu wajen rage yawan kudaden da gwamnati za ta kashe domin siyawa shugaban kasa da mataimakinsa sabbin jirage.

DUBA WANNAN: ‘Yan Majalisa Sun Bukaci FG Ta Gaggauta siyawa Tinubu da Shettima sabbin Jirage

Majiyar ta kara da cewa gwamnati ta yanke shawarar siyar da tsofin jiragen ne saboda a halin yanzu babu isassun kudi a lalitar gwamnati da za a yi amfani da su domin siyen sabbin jirage ga Tinubu da Shettima.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni kamfanin dillanci na JetHQ ya kawo tayin siyan jiragen da mutane uku suka yi zuwa ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Zakari Mijinyawa, mai magana da yawun Nuhu Ribadu ya tabbatar wa da manema labarai cewa akwai maganar siyar da jiragen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories