Jajircewa Da juriya ya sa Ɗan Najeriya Emmanuel Oluwasayomi Ahmadu ya sami lambar girmamawa biyu a ƙasar Amurka inda a halin yanzu yake karatun digirinsa.
Labarin jajircewa da juriyar Emmanuel ta kasance wani bangaren da ya samo asali sakamakon juriya da hakuri.
Sanuwar Emanuel idon duniya ya samu asali ne a shekarar 2018 lokacin da ya lashe lambar yabo ta ƙasa da ƙasa na yammacin Afirka yayin da yake karatun digiri sa na farko a Jami’ar Benin (UNIBEN).
Babban abin mamaki game da Emanuel shi ne irin yadda tun tasowar sa ya fuskanci ƙalubalen rayuwa wanda har haka ta sa ya yi tsalle-tsallen karatun firamare , Emanuel Sai da halarci makarantun firamare ɗai-dai har guda 16 makarantun sakandare 14 saboda halin rayuwa.
A cigaba da gwagwarmayar karatu sai da Emmanuel ya shafe shekaru biyar yana zana jarrabawar O’level a lissafi ya yi zaman jarabawar sau 17 kenan .