Barayi Sun Balle Masallaci Sun Kwashe Batiran Sola A Kano

Wasu batagari, da ba a son ko su waye ba ya zuwa wannan lokaci, sun balle wani Masallaci a birnin Kano tare da yin awon gaba da baturan sola da ake amfani da su a Masallacin domin samar da wutar lantarki.

An yi kiyasin cewa darajar batiran da aka sace ya haura Naira dubu dari uku, N300,000.

WikkiTimes ta rawaito cewa wani mutum mai suna Ibrahim Bala Aisami shine ya sanar da faruwar lamarin a shafinsa na dadalin sada zumunta na ‘Facebook’, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Masallacin dake jikin gidansa.

“Wasu barayi sun balle tagar Masallacin da ke gidana sun shiga har ciki sun balle wurin da aka kawwame batiran sola sun kwashe su. Kudin Batiran ya haura N300,000.

DUBA WANNAN: Kano: Mutumin da ya cinnawa Masallaci wuta ana tsaka da Sallah ya shiga hannu

“Muna rokon jama’a su tayamu addu’a Allah ya tona asirinsu ya kuma bamu ikon maye gurbin batiran da aka sace domin mu cigaba da aiyukan ibada cikin kwanciyar hankali,” kamar yadda Aisami ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Yunkurin samun karin bayani ko kuma jin ta bakin rundunar ‘yan sanda a kan faruwar lamarin bai yiwu ba har zuwa lokacin wallafa wannan labari.

WikkiTimes ta fahimci cewa Masallatan birnin Kano da suke amfani da sola suna kebe batiransu ta hanyar yi musu kariya a cikin akwatin karfen rodi don gudun satar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories