Kusan Mutum 400 Aka Kashe A Farkon Kwanaki 100 Na Gwamnan Filato A Mulki

A kwanakin baya ne Gwamna Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP, ya cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin jihar, a wani matakin da za a iya cewa farawa da rashin sa’a, a karkashin mulkinsa rahotonni daban-daban sun yi nuni da cewa an samu kashe-kashe da ya janyo mutuwar kusan mutum 400 a farkon kwanaki 100 na mulkin sabon gwamnan.

A wani binciken da ‘WikkiTimes Hausa’ ta gudanar ya nuna mata cewa, wannan adadin duk da an fara kiyasce su ne tun a watan Afrilu wata guda kafin a rantsar da gwamnan, amma bincike ya nuna cewa mafi yawan kashe-kashe da hare-haren da aka kai din sun fi aukuwa ne a watan Mayu, Yuni da Yuli lokacin da gwamnan ke kan mulki.

Jihar Filato dai ta jima tana samun matsalolin rikice-rikice da ke janyo mace-macen rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tursasa ma wasu dubban mutane yin gudun hijira domin neman tsira da rayukansu kamar yadda binciken WikkiTimes Hausa ya gano.

Shi dai sabon gwamna, Caleb Mutfwang, a lokacin amsar mulki, ya yi alkawarin hada kan al’ummar jihar ne, sai ya yi gargadin masu kunna wutar rikici da raba kawukan jama’a da cewa daga yanzu su daina domin shi kam ba zai lamunci hakan ba.

Sai dai za a iya cewa gargadin nasa bai yi tasiri ba, domin kuwa an samu kashe-kashe a cikin kwanakinsa 100 na mulki.

A fadin gwamnan, ya kamata ne kowa ya bada gudunmawarsa wajen kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar ba tarwatsawa ba.

Ya koka kan yadda gwamnatin da ya amshi mulki a hannunta, ta gadar wa gwamnatinsa tulin basuka da suka haura sama da biliyan N200.

“Ba za mu tozarta kowa ba, kuma ba za mu zauna muna sukar juna ba, za mu yi zurfin tunani ne mu dauki matakin gyara abubuwan da muka gada yau, amma muna bukatar mu yi wasu tulin tambayoyi, saboda muna bukatar ne mu yi aiki tukuru mu kafa tarihi wajen kyautata mulki,” ya shaida.

A ranar Alhamis 13 ga watan Yulin 2023, wata kungiyar kare hakkin bil-adama ‘Gideon and Funmi Para-Mallam Peace Foundation’ ta yi zargin cewa, a kalla mutum 346 ne aka kashe cikin watanni uku a kananan hukumomi takwas na jihar Filato.

Kungiyar ta ce, daga cikin wannan adadin, sama da rayuka mutum 200 ne suka salwanta a rikice-rikicen da aka samu a karamar hukumar Mangu kawai zuwa ranar 8 ga watan Yulin 2023.

Babban daraktan gidauniyar, Rabaran (Dakta) Gideon Para-Mallam, shi ne ya shaida wannan adadin a wani rahoton da ya fitar wa ‘yan jarida a Abuja, inda ya ce, wadannan kashe-kashen sun faru ne a tsakanin ranar 17 ga watan Afrilun zuwa 10 ga watan Yulin 2023, kuma a halin yanzu sama da mutum 18,751 ne suke gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira 14 da ke jihar Filato.

Para-Mallam, dan rajin tabbatar da zaman lafiya, ya kara da cewa, mutum 17 an kashe su ne a Bokkos, Mangu 234; Barkin Ladi 39; Riyom 36; Jos ta arewa 5; Jos ta arewa 9; Mikang 5 da kuma Bassa 01.

Yawan kashe-kashe a jihar da ya sake kunno kai lamarin da ke kara barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar jihar da jihohin da ke makwaftaka, a cewar rahoton binciken WikkiTimes Hausa.

Bisa zallar bayanan da kungiyar cigaban kabilar Mwaghavul (MDA) da kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) suka bayar a watan Yulin da ta gabata, sama da mazauna kauyukan Mangu da wasu Fulani sama da 200 ne aka kashe a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2023 lamarin da ke kara jefa jama’a cikin zaman dar-dar.
Kodayake, a wata tattaunawa mai magana da yawun gwamnan jihar Filato Gyan Bere, ya ce gwamnati ba ta samu rahoton yawan mutanen da aka kashe a rikicin na baya-bayan nan ba.

“Abin da na sani shi ne mutanen Mangu na cikin hali maras kyau. Ni na san da cewa ana kashe-kashe a Mangu, ana yi wa mutanen kwantar vauna ana kashe su.”

Zuwa watan Yulin, rikicin da ke faruwa a Mangu dai ya sanya gwamnatin jihar ta kakaba dokar hana fita karo biyu cikin wata uku kacal da suka gabata.

Idan za a iya tunawa ma, a cikin watan Mayu ma gwamnatin Filato ta kakaba dokar hana fita a yankin na Mangu, bayan wasu hare-hare na ‘yan bindiga kaddamar lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama da lalacewar kadarori hade da sanya mutane da dama sauya muhallai. 

Mazauna Mwaghavul, al’ummar da ta yi fice a harkar noma a karamar hukumar Mangu sun shaida wa cewa maharan sun kutsa cikin kauyukansu inda suka bude wuta kan mutane tare da cinna wa gine-gine wuta.

A gefe guda, an zargi jami’an tsaron jiha ‘Operation Rainbow’, sun mamayi ruggan Fulani da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato tare da banka wa gidaje da dama wuta.

Fulanin sun ce rundunar ke kai musu hare-hare da kona musu gidaje da bunkuna. 

Fulanin sun ce ba za su iya kiyasce adadin wadanda suka jikkata ba, ko gidajen da aka kona ba, inda suka ce wasu mutane ma sun mutu a harin.

A cewar Fulanin, jami’an sun shiga yankunan wajajen karfe 5 inda suka fara harbi kan mai-uwa-da-wabi, tare da bude wuta a kan gidajensu tare da Armoured Personnel Carrier (APC) lamarin da ya janyo konewar gidajensu da dama.

Sai dai kuma, ko’odinetan jami’an tsaron, Sitdang Mungak, ya karta zargin tare da cewa labarin shaci fadi ne kawai.

Sai dai kuma, shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Nuru Abdullahi a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki kwararan matakan shawo ka lamarin domin guje wa lamarin ya kazanta.

“Muna da kwarin guiwar cewa gwamnatin jiha ba za ta iya shawo kan wannan matsalar ba. Jami’an rundunar Rainbow da ‘yan daba suke jagoranta sun kona gidaje, kuma asalin manufarsu shi ne su fitar da mu daga Filato gaba daya.

“Mambobinmu da suke Sarpal, Kombun, Rinago, Dtmirle, Kangang, Aloghom, Fongon, Bongangida, Luggere, Gaude, Jwaksham, Borwa, Luggadimesa, Tidiw, da wasu wuraren su ma an kona musu muhallai. Kan hakan, muna kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ceto mu daga wannan halin da muke ciki,” ya shaida.

Isa Ibrahim Jamo, daya ne daga cikin al’ummar yankin da lamarin ya shafa, ya zargi jami’an da kona gidaje a Changal, Kombili, Lamor, Washina, Gayam, Anguwan Baraya, Vivim da wasu yankuna na Jannaret.

“Kadarorinmu da suka hada da kayan sawa, katifu, takin noma, abinci dukka sun kone. Mata da yara sun gudu zuwa kauyukan Gindiri da Kasuwan Ali domin fargabar abun da ka iya sake faruwa,” Jamo ya shaida. 
Sai dai mazauna Mwaghavul ‘yan asalin karamar hukumar Mangu sun zargi Fulani da cewa suna ta kokarin mayar musu da muhallai zuwa wuraren kiwonsu a kokarunsu na malleke wa jama’an yankin filaye.

Kungiyar ‘yan kabilar ta kuma karyata zargin da Fulani suka yi na cewa jami’an rundunar Rainbow sun kai musu hari tare da kona wa mambobinsu wurare.

Shugaban kungiyar cigaban Mwaghavul (MDA), Chief Joseph Gwankat, ya ce, “Mun fito ne domin mu shaida muku hakikanin abubuwan da suke faruwa da muhallanmu. Wasu ‘yan ta’adda na kai hare-hare a Mwaghavul da wasu sassan karamar hukumar Mangu.

“Al’ummar Mwaghavul mutane ne masu son zaman lafiya kuma suna zaune da makwabtansu lafiya. Har zuwa lokacin da Fulani suka kutso kai suke kokarin mamaye mana wurare. 

“Hare-haren da Fulani suke kawo mana ya fara ne tun a watan Afrilu har zuwa yanzu, da farko lamuran sun fara ne da garkuwa da mutane, lalata gonakai da wasu matsaloli daga baya lamarin ya zama kaddamar da hare-hare.”

“Abun takaici, wadanda suke kashe mu, su kashe mana jama’a sune kuma suke ta korafin wai ana kona musu muhallai.

“A gundumar Bwai garuruwan da suka kunshu: Murish, Dungmunan, Kubat, Tim Naanle, Pil, Fungzai, Manja, da Chisu.m an kashe mutum 70. A gundumar Kombun: Fungkipang, Nting an kashe mutum 5. Gundumar Mangu a garuruwan da suka shafi: Jwaktumbi, Kantoma, Mangul, Alohom 1, Alohom 2, Gongon, Dan Hausa, Kikyau 1 da 2, Gudum, Tyop, Kwaskipanleng, Gaude, Bure, da Ntam, mutum 70 nan ma aka kashe.

“Gundumar Panyam: Changal, Kombili, Washna, Jwak Chom, Larkas, Fushi, Kwahas, Dangdai, Atuhun, Adep, Ajing, Daika, Dikong, Lakopal, Kogul, and Niyes, aka kashe. A gundumar Pushit: Lakasi, Gwet 2, Gwet 1, Mutong, Keptul, Gung, Pyantuhul, Kus Hi, Nbwor, Vodni, Pwaskop, and Nten an kashe mutum – 17. Gundumar Kerang: Konji, an kashe mutum 8,” ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories