Ajali: Babban Jami’in Kwastan Ya Yanke Jiki Ya Fadi Babu Rai A Zauren Majalisar Wakilai

Essien Etop, babban jami’i mai mukamin mataimakin shugaba mai kula da sashen gudanarwa da aiyuka na musamman a hukumar kwastam (NCS), ya yanke jiki ya fadi babu raia zauren majalisar wakilai a ranar Talata, 25 ga Watan Yuni.

Lamarin ya faru ne a yayin da Essien ke amsa tambayoyin ‘yan majalisa bayan da ya kammala gabatar da jawabi a gaban ‘yan majalisar da ke bin ba’asin yadda hukumar kwastam ke gudanar da aiyukanta.

Yana cikin amsa tambayoyin ne sai ya yi tari kafin daga bisani ya yanke jiki ya fadi, lamarin da yasa aka garzaya da shi zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin hukumar kwastan, Honarabul Bamidele Salam, ya ce kwamitinsa zai dakatar da aiyukansa na tsawon sati guda domin juyayin mutuwar Mista Essien.

DUBA WANNAN: Yadda Tsananin Zafi Ke Barazana Ga Lafiya Da zama Lafiya

“Bamu ji dadin faruwar lamarin ba. Mutum ne da ya fahimci aiki, shi yasa ma har aka turo shi ya wakilci hukumar kwastam wajen bayar da bayani a kan aiyukan hukumar su,” kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito cewa Honarabul Bamidele ya fada.

Ya kara cewa, “ya katse magana tare da bayyana cewa yana bukatar ruwan sha, har muka yi masa raha da cewa ko yana son shan shayi ne.

“Bamu ji dadin abinda ya faru ba. Kwamitin mu ya dakatar da aiyukansa na tsawon mako guda domin juyayin rasuwar babban jami’in.”

Kazalika, shugabanj majalisar wakilar, Tajuddeen Abbas, ya bayyana kaduwarsa tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalin Mamacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories