Shugaban EFCC Ya Bada Umurnin Damƙe Jami’an Da Suka Kutsa Dakin Otel A Legas

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin kama wasu jami’an hukumar su biyu da aka kama da laifin kutsawa tare da cin zarafin wata ma’aikaciyar Otel din Regional Otel, Ojo, a garin Legas.

 A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana a yanar gizo, an ga jami’an hukumar da suka sanye da kayan gida sun shiga ɗaya daga cikin dakunan otal din.

A lokacin da lamarin ya faru a bidiyo an ga wata ma’aikaciya da sunan ta bai bayyana ba a otal din tana ƙoƙarin bude kofar daga ciki inda su kuma jami’an suka yi amfani da karfi suka bude kofar.

 Bayan sun shiga sai aka ga daya daga cikin jami’an yana marin matar kafin daga bisani ya umarce ta ta fice daga dakin.

 An samu Bidiyo faruwar lamarin ne a CCTV.

 A cikin jawabinsa, Oyewale ya ce lamarin ya faru ne a wani samame da aka kai da sanyin safiyar yau. Ya ce, samamen ya kai ga kama mutane da dama.

 “Haka kuma Shugaban na EFCC ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abinda ya faru a otal din tare da tabbatar da cewa za a dauki matakan ladabtarwa a kan duk wani jami’in da aka samu da laifi,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories