Kano : Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Musanta Alaƙa Da Aminu Ado Bayero

 Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Salman Garba, ya ƙaryata ikirarin da ke yawo cewar yana da alaƙar ya uwa taka da hamɓararren sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, 

Ya jaddada aniyarsa na yi wa duk mazauna yankin hidima ba tare da nuna son kai ba, ko wariya ba,ba tare da la’akari da addini, kabila ko kuma asalin ba.

Kwamishina Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawar farko da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano a jiya Laraba.

Haka kuma Ya jaddada muhimmancin daukar tsauraran matakai wajen yaƙi da miyagun laifuka, tabbatar da doka da oda da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

 ” Tsaron rayuka da dukiyoyi shine babban abin da muka sa a gaba, kuma za mu yi amfani da duk abinda doka ta tanadar , cewar Kwamishinan.

“Ni dan Najeriya ne, kuma labarin da ke yawo cewar ina da dangantaka da tsohon sarki Aminu Ado Bayero Manzon kurege ne; Ba Gaskia ba.  Aikinsa shi ne In tsaya tsayin daka wajen yiwa Kano hidima gwargwadon iko,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories