N50,000 Ake Biya Na Duk Lokacin Da Na Yi Safarar Makamai Zuwa Wurin ‘Yan Bindiga – Aisha Abubakar

Wata mata da jami’an rundunar ‘yan sanda suka kama da carbin alburusai 550 na bindigar AK47 ta bayyana cewa ana biyan ta Naira dubu hamsin duk lokacin da ta yi safarar alburusai zuwa ga ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Matar, mai suna Aisha Abubakar, ‘yar shekara 25, ta fada komar rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a tsakanin Kaduna zuwa Zaria yayin da take kan hayarta ta zuwa Katsina daga garin Loko a jihar Nassarawa a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, 2024.

Aisha ta yi magana da manema labarai yayin da rundunar ‘yan sanda ta yi bajakolin masu laifi a hedikwatar ta ranar Alhamis.

“Jami’an ‘yan sanda sun kama ni da alburusai. Da farko wani ne mai suna Wawo ya kawo min buhun taki ya ce na tura Katsina ta hanyar bawa wani direba.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda Buharin Yadi a Katsina

“A karo na biyu kuma da kaina na je har Katsina na kai makaman. A zuwana na uku ne ‘yan sanda suka kama ni. Ana biya na N50,000 kowacce tafiya,” a cewar ta.

Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar gano alburusan ne a wani binciken kayan matar da aka yi.

Da farko wacce ake zargin ta musanta aikata safarar kafin daga baya ta amince da aikata wannan laifi.

Kwamishinan ‘yan sanda, Ali Audu Dabigi, ya bayyana cewa bayanan da Aisha ta bayar dangane da masu bata makamai ya kai ga, ya zuwa yanzu, an kama wasu mutane biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories