Tinubu, Gwamnoni Sun Yi Biris Da Maganar Mafi Ƙarancin Albashi 

Har yanzu babu wani batu da aka ji game da mafi ƙarancin albashi daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnonin jihohi 36 bayan zaman ganawa da majalisar tattalin arziki da ya gudana a jiya (NEC).

 Miliyoyin ƴan Najeriya da ƴan kungiyar ƙwadago sun yi tsammanin cewa gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi za su cimma  matsaya kan lamarin, wanda aka ɗaɗe ana cin ƙwan makauniya akan sa tun bayan cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023, wanda shine ranar da Tinubu ya karbi mulki, kuma karshen wa’adin mafi ƙarancin albashi na N30,000 da aka amince da shi a shekarar 2019.

Taron na NEC wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranta, ya samu halartar shugaba Tinubu a jiya, wanda lamarin ya kara sanya masu lura da al’amura fatan ganin cewa akwai yiwuwar cimma matsaya game da lamarin  .

 A kwanakin baya ne, kwamitin wakilai 37 kan mafi karancin albashi na kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata na tarayya, Bukar Aji, ya mika wa shugaba Tinubu Rahoto game da abinda ake buƙata akan mafi ƙarancin albashi makonnin da suka gabata, bayan shafe kusan watanni biyar ana zama.

In ba Manta ba dai makonni da suka shige ƙungiyar kwadago ta tsunduma Yajin aikin gama gari akan ƙarin mafi ƙarancin albashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories