Mamakon Ruwan Sama Da Iska Sun Rushe Gine-Gine Da Hallaka Mutum 8 A Kano, 1 A Yobe

Ana kyautata zaton a ƙalla mutane takwas sun rasa rayukansu bayan rugujewar wani ginin bene a unguwar Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Lamarin ya afku ne yayin da Leburori ke tsaka da aikin ginin a safiyar ranar Juma’a.

Majiyoyi sun bayyana cewa aƙalla mutane 15 al’amarin ya rutsa da su ciki har da Mamallakin ginin wanda aka bayyana cewa sunansa Sharu, magina da Leburori, masu fakewa a ginin saboda ruwan da kuma masu wucewa ta hanyar lokacin da ake tafka mamakon ruwan saman da sanyin safiyar ranar Juma’a.

Bayan samun wannan labari ne, matar Sharu ta yi gaggawar zuwa inda lamarin ya faru, sannan ta nemi a kawo agaji. An roƙi makwabta da mutanen da ke tsaye a wurin da su agaza a ceto wadanda ɓaraguzan gini suka danne.

An garzaya da mutum 7 zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, inda mutum ɗaya ya rasa ransa a hanya.

Majiyoyin mu sun shaida mana cewa wadanda suka jikkata suna karɓar kulawa ta musamman a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad.

KARANTA: Tirela Ta Kwace Ta Kutsa Kai Cikin Masu Sallar Juma’a A Kano

A wani rahoton mai kamanceceniya da wannan, an tafka mamakon ruwa da guguwa mai ƙarfin gaske wadda suka yi sanadiyyar rasuwar wani yaro mai shekaru 7 kacal a duniya a Tsohon Garin Nangere da ke Ƙaramar hukumar Nangere a Jihar Yobe.

A cewar gidan talabijin na NTA, ruwan wanda ke haɗe da guguwa yayi sanadiyyar jikkata mutane 20,ruguza gidaje da shaguna 50 da kuma hallaka yaro ɗan shekera 7.

Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories