Masarautar Bauchi Ta Kori Masu Sarautun Gargajiya 6

Masaraurar Bauchi ta warware naɗin sabbin masu Sarautun Gargajiya shida (6) a gundumar Galambi da ke ƙarƙashin masarautar.

Wannan bayanin na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwar mai ɗauke da sanya hannun babban jami’in watsa labarai na masarautar Bauchi, Malam Babangida Hassan Jahun, da aka aike da kwafinta wa ‘yan jarida a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, wannan matakin, masarautar ta ɗauka ne a yayin zamanta da ta gudanar.

Masaraurar ta ce, a bisa haƙiƙanin zance matakai da hanyoyin da babban Hakimin Galambi ya bi wajen wankan sarautar masu Sarautun gargajiyan ya saɓa wa ƙa’idoji da tanade-tanaden irin wannan naɗin.

Wakilinmu ya yi labarto cewa Hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba, wanda shi ne Danlawal ɗin Masarautar Bauchi ya naɗa tare da wankan sarauta ga mutum shida suka kasance hadimai a fadarsa da suka haɗa da Galadiman Danlawal, Majidadin Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal, Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal gami da Hardon Danlawal.

Bugu da ƙari, masarautar ta Bauchi ta kuma dakatar da haramta wa hakimin Galambi naɗe-naɗen masu Sarautun gargajiyan na tsawon shekara guda da zai fara aiki daga ranar 7 ga watan Nuwamban 2023.

Don haka daga yanzu, hakimin wanda shigo ne a masarautar Bauchi bai da damar naɗi har na tsawon shekara ɗaya.

Sannan, sanarwar ta ce, dukkanin wasu hanyoyin da za a bi wajen naɗin Sarautun gargajiyan dole ne ya kasance an bi dokoki da ƙa’idoji da masarautar Bauchi ke tafiya a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories