Shugaban ‘Yan Bindiga Ya Yi Alkawarin Bawa Manoma Kariya Daga ‘Yan Ta’adda A Zamfara

Mazauna yankin Magami dake karkashin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun shiga cikin rudani bayan sanannen shugaban ‘yan bindiga, Dogo Gide, ya yi musu tayin cewa zai basu kariya.

Gidan Talabijin na Channels24 ya rawaito cewa Dogo Gide ya sanar da mazauna yankin cewa zai basu kariya tare da sanar da manoma cewa su fita su noma gonakinsu ba tare da tsoro ko wata fargabar cewa za a sacesu a yi garkuwa da su ba.

Sai dai, mutanen yankin da kewaye sun kalli wannan tayi na Dogo Gide ta mabanbantan fuskoki.

Rahotanni sun bayyana cewa a ‘yan kwanakin baya bayan nan Dogo Gide ya yi hijira zuwa kauyen Kizara mai makwabtaka da Magami bayan ya sha da kyar yayin wani artabu da dakarun soji a dajin Madada dake karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin masaurautar Dansadau da ya nemi a boye sunansa ya sanar da Channels Television cewa koda Shugaban ‘yan ta’addar zai iya bayar da wata kariya za ta kasance ta wucin gadi ne kawai.

Mazauna Masarautar Dansadau sun nuna rashin amincewa da batun yin sulhu da ‘yan ta’adda ko barin tsaronsu a hannun shugabannin ‘yan bindiga tare da yin kira ga hukuma ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin da jihar baki daya.

DUBA WANNAN: Luguden wutar NAF Ya Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 80 A Katsina

Jami’in yada labarai na rundunar Hadarin Daji, Kaftin Suleiman Omale, da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, sun sanar da Channels cewa basu da masaniya a kan dawowar Dogo Gide zuwa kauyen Kizara.

Sai dai, ASP Yazid ya kara da cewa zai tuntubi babban jami’in rundunar ‘yan sanda mai kula da ofishinsu na Dansadau domin neman karin bayani

“Bani da wannan bayanin amma zan tuntubi DPO din Dansadau, za ku ji daga gare ni,” ASP Yazid ya shaidawa wakilin Channels.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories