Ƴan Siyasar Arewa Sun Watsawa Mutane Ƙasa A Ido – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsaƙiya, Shehu Sani, ya danganta matsalar tsaro da tattalin arzikin da ke addabar yankin Arewa ga ƴan siyasar yankin.

 Shehu Sani, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, ya ce ƴan siyasar yankin Arewa ba su yi amfani da karfin kujerun su ba wajen amfanar al’ummar su.

 A cewarsa, duk al’amuran da ke faruwa a Arewa sun faU ne“sakamakon rashin samun ingantaccen shugabanci” a yankin.

“Kun ga Ni ɗan Arewacin Najeriya ne ɗan Jihar Kaduna, kuma idan akwai wani wuri, da zan so in ga ci gaban sa da jama’a suna zaune lafiya, da samun damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum,shi ne inda na fito.  ” cewar Shehu Sani

Shehu Sani ya cigaba da cewa duk da irin ƙarfi da ƴan Arewa suka yi a siyasa amma duk da haka yankin na fama da matsalolin rashin tsaro, talauci, da yaran da ba sa zuwa makaranta .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories