Sarkin Damaturu Ya Umurci Ƴan Kasuwa Da Su Rage Farashin Kayan Masarufi

Sarkin Damaturu, Dr Shehu Hashimi II Ibn Umar El-Kanemi, ya yi kira ga ƴan kasuwa da su dubi Allah su tausaya wa talakawa su rage farashin kayayyakin abinci a jihar duba da irin yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar.

Sarkin wanda ya nuna damuwarsa kan yadda farashin kayayyakin masarufi ke cigaba da yin tsada sosai wanda hakan ke ba mai karamin ƙarfi wahalar siya.

 Sarkin ya yi wannan roƙon ne a fadarsa da ke garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe,inda ya ce ƴan Najeriya na matuƙar shan wahalar rayuwa sosai.

Ya ce, “Akwai bukatar a yiwa manyan ƴan kasuwa kiran gaggawa da su yi haƙuri su rage farashin kayayyakin abinci domin samun sauki ga talaka.

 Haka kuma ya buƙaci ƴan kasuwa a jihar da su yi duk yadda za su don ganin an rage farashin kayan masarufi domin amfanin jama’a da kuma taimakawa marasa galihu.

Ya kuma shawarce su da su binciki duk hanyoyin da suka san za a samu sauƙin farashi don sauƙaƙawa talakawa ba tare da sun yi asara ba .

 Sarkin ya kuma bukaci ƙungiyoyi da su kara ƙoƙari wajen ganin an taimaka wa nakasassu da kuma masu ƙaramin ƙarfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories