Sinadari Mai Fashewa Ya Tashi A Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Da Ke Zungeru Dam

An samu fashewar wani sinadari a cibiyar samar da wutar lantarki da ke Zungeru Dam a jihar Neja tare da jikkata mutane da dama da kuma lalata kayayyakin samar da wutar lantarki.

A cewar wani shaidar gani da ido, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin kuma mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar sinadarin da ya zuwa yanzu ba a tabbatar da menene ba.

SaharaReporters ta rawaito cewa wani injiniya dan kasar China da ke aiki a cibiyar ya samu munanan raunuka a kansa da hannayensa, lamarin da yasa aka garzaya da shi babban asibiti dake Minna, babban birnin jihar Neja.

Wata majiyar ta sanar da SaharaReporters cewa ana shirin mayar da Injiniyan zuwa asibitin kwararru na IBB domin bashi kulawa ta musamman.

DUBA WANNAN: Kano: Mutumin da ya cinnawa Masallaci wuta ana tsaka da Sallah ya shiga hannu

Ya zuwa yanzu ba a bayyana abinda ya haddasa tashin sinadarin. Kazalika, babu wani jawabi a hukumance da aka fitar dangane da fashewar sinadarin.

SaharaReporters ta wallafa cewa ta yi yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, domin tabbatar da faruwar lamarin amma hakan bata samu ba saboda bai amsa kiran waya ba kuma bai bayar da amsar sakon da aka aika masa ba.

Akwai fargabar cewa fashewar sinadarin za ta iya shafar samar da wutar lantarki a wasu sassan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories