Ƴan Bindiga Sun Bindige Malamin Jami’ar FUDMA, Sun Yi Awon Gaba Da Ƴaƴansa 2

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe Dokta Tiri Gyan David malami a jami’ar gwamnatin tarayya Dutsinma, FUDMA a jihar Katsina, tare kuma da yin garkuwa da ‘ya’yansa biyu.

 Rahotanni sun bayyana cewa an kashe malamin ne da sanyin safiyar yau Talata a gidansa da ke unguwar Yarima quarters a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

 Marigayin dai kafin rasuwar sa ya kasance shi ne shugaban sashin tattalin arziki, noma,da raya karkara na jami’ar .

Majiyoyi sun ce ƴan bindigar sun mamaye yankin ne da manyan makamai, inda suka rika harbi ba ƙaƙautawa don tsorata mazauna wurin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.Tare kuma da bada tabbacin rundunar za ta fitar da cikakken bayani game da abinda ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories