Ambaliyar Ruwa Ya Yi Ajalin Wani Ɗalibi A Jihar Legas

Joshua ɗalibai ɗan aji shida a firamari ya gamu da ajalin sa a hanyar sa ta dawowa makaranta sakamakon Ambaliyar ruwan sama da ya afku a yankin Ketu jihar Legas.

 Da take mayar da martani game da lamarin mahaifiyar Joshua, mai sayar da ’ya’yan itace, ta yi kuka,ta kuma nuna baƙin cikin ta game da rashin ɗanta tilo.

KU KARANTA :

 “Joshuwa ya mutu sakamakon tsananin yunwa da sanyi.  Ya na aji shida ne har sun kusa fara rubuta jarrabawar gamawa,” inji mahaifiyar mamacin.

 Mahaifiyar Joshua ta matuƙar nuna damuwanta inda ta bayyana cewa bai dade ba ta rasa gidanta sakamakon gobara .

 Ta roki jama’a da su taimaka mata ta nemo inda ruwa ya tafi mata da ɗan ta inda ta yi alkawarin yin duk wani abu don dawo da shi.

 Wani shaida, wanda kuma shugaban matasa ne a yankin, mai suna Oloyede, ya ce lokacin yana dawowa ya haɗu da yara a inda ya gargaɗe su da su yi hankali domin hanyar batada kyau.

Wani shugaban al’ummar yankin a nashi albarkacin bakin ya zargi gwamnati da yin watsi da aikin samar da magudanar ruwa a yankin wanda hakan ne ya janyo yankin ke fama da Ambaliyar Ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories