KADUNA: ‘Yan Bindiga Sun Saki Babbar Alkaliya, Sun Rike ‘Ya’yanta Uku

‘Yan bindiga sun saki wata babbar Alkaliya, Janet Gimba, wacce ke jagorantar kotun gargajiya da ke unguwar Sabo a cikin garin Kaduna, bayan yin garkuwa da ita tare da ‘ya’yanta guda uku.

Musa Gimba, miji ga alkaliya Janet, shine ya tabbatar da hakan, kamar yadda sashen Hausa na muryar Amurka ya wallafa.

Gimba ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun cigaba da tsare ‘ya’yansu Uku duk da sun saki Mahaifiyarsu, Janet.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun bukaci naira miliyan N150 a matsayin kudin fansa kafin su saki Yaran tare da yin barazanar zasu kashe su idan ba a biya kudin ba a cikin kwanaki uku.

DUBA WANNAN: Karin Bayani: Jirgi Ne Mai Sarrafa Kansa Ya Yi Hatsari – NAF Ta Yi Karin Haske

‘Yan bindiga sun sace Alkaliya Janet tare da ‘ya’yanta a ranar 24 ga watan Yuni a gidansu da ke unguwar Mahuta a yankin karamar Chikun.

Mansir hassan, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikin ‘ya’yan Alkaliyar mai suna Victor Gimba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories