Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Yi Korar Ma’aikata

Hukumar ma’aikata ta jihar Bauchi ta bayyana korar ma’aikata su huɗu sakamakon saba ka’idojin aiki a wasu ma’aikatu na jihar (MDAs).

 Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin hakan ya zama izina ga sauran mutane don tabbatar da ɗa’a da kuma ladaftar da ma’aikata wajen bin ka’idojin aiki.

KU KARANTA :

 Shugaban hukumar Alh Abubakar Usman shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ake yi na manyan jihar mai taken ‘Actualizing My Bauchi Project’ da nufin samar da bayanai kan ayyukan gwamnatin jihar Bauchi da kuma Ma’aikatu.

Shugaban ya cigaba da cewa wadanda aka kora sun fito ne daga ma’aikatar hukumar fansho ta jihar, ma’aikatar kudi, da kuma hukumar kula da asibitocin jihar sakamakon kama su da laifin ƙarya da kuma damfara .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories