Gwamnatin Kano Zata Biya Bashin Ƴan Fansho Gaba ɗaya

A zaman da majalisar zartarwar jihar ta gudanar a jiya laraba karkashin jagorancin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, majalisar zartarwar ta amince da abubuwa kamar haka:

1- Saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar.

2- Naɗa kwamiti na musamman don duba yadda za a biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.

3- Za’a gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami’ar Bayero dake Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimin addini ta Malam Aminu Kano haɗi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa’adatu Rimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories