Matar Da Za A Yi Wa Dashen Koda Na Neman Taimakon Miliyan 20

Misis Odubiro Adebisi, ‘yar kimanin shekara 60 daga garin Ijebu-Ode a jihar Ogun, ta roki ‘yan Najeriya da su taimaka mata da kudi naira miliyan 20 domin yi mata dashen koda.

Rahoton likitan Adebisi, ya fitar a lokacin da yake zantawa da WikkiTimes daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Babcock, ya nuna cewa an ba ta gado (CKD) domin tana buƙatar sai an yi dashen koda.

Rahoton mai kwanan watan 4 ga watan Satumba 2023, ya bayyana cewa “mai jinyar tana fama da matsalar hawan jini shiyasa aka tura ta zuwa wurinmu saboda tana fama da amai, rashin karfin jiki, ciwon ciki, da wahalar fitar numfashi.

“Sannan akwai rama a tattare da ita da kuma rashin fitar fitsari.

“Har ila yau, akwai kumburi da kuma rashin jini wanda saida aka mata karin jini.”

“lamarin ta ya tsananta inda har ya kai mataki na biyu wato Chronic glomerulonephriti da kuma uremic encephalopathy,” rahoton likita na Adebisis ya bayyana hakan. 

Rahoton ya kara da cewa Misis Adebisi za ta bukaci wankin koda da kuma dashe tare bukatar gwaje-gwaje kafin a yi aiki da kuma bayan an yi aiki.

Rahoton ya kuma kara da cewa za a bukaci kusan naira miliyan 20 da kuma magunguna bayan an yi tiyatar.

Bugu da kari, a wata wasika da dangin Adebisi suka rubuta domin neman tallafi, an bayyana cewa likitan ta ya ba ta shawarar ta je a yi mata dashen koda, inda ta kara da cewa gwajin da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa kodar ta biyu ba sa aiki yadda ya kamata.

“A cikin ‘yan watannin da suka gabata, lafiyarta na kara tabarbarewa, kuma bayan tuntubar likitoci da gwaje-gwaje an tabbatar da cewa tana bukatar agajin gaggawa a kan ciwon nata.

“Rashin lafiyar ta ya sa duk abun da muka mallaka ya kare, saboda jinyar yana bukatar kudi sosai.

“Tsarin yadda zai kasance sun haɗa da dashen koda, ba wai aikin ne kadai ke da tsada ba har kudin kafin yin aiki, kulawa bayan tiyata, magunguna, da kuma ci gaba da ganin likita.

“Yana yin tsadar abubuwa shi ya sa ba za mu iya mu kadai na shiyasa muke fito neman taimako.”.

Danta, Mista David Adenuga, wanda ya yi magana a madadin iyalan Adebisi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su taimaka musu a cikin wannan hali da suke ciki.

“Duk kankantarsa ba za mu raina ba domin tallafin da kuke bayar wa zai taimaka mata wajen ganin ta samu muhimman kulawar jinyar da take bukata.

“Tallafin kudi ga Adebisi”za ai mata dashen koda ku na iya aikawa zuwa asusunta na First Bank: 3050472812 tare da asusun Odubiro Marian Adebisi da kuma na danta David Adenuga, wakilin jaridar The Nation da ke Bauchi kuma za a iya tuntubar ta a wannan lambar 09024203369.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories