Hanyoyin Kare Kai Daga Matsalolin Hanta (Liver Problems)

Kare kai daga matsalolin hanta abu ne da ya kamata domin ita hanta tana cikin gaɓɓai na musamman (vital organs) da suke tafiyar da rayuwar ɗan Adam.

Ita ke tace gurɓatattun sinadarai daga jiki, sarrafa sinadarai da jiki ke bukata da magunguna in mutum yasha. Aikin ta na da yawa.Abubuwan lura domin kare hanta daga samun matsala:

1. A gujewa shan magunguna ba tare da cewa masana ne suka ce a sha ba, sannan asha yadda suka ce asha. Misali; Paracetamol maganin zazzaɓi ne da zafin jiki/ciwon kai, hanta take sarrafa shi. A lokacin da mutum ya tsira shan shi kullum ba bisa ka’ida ba, zai kasance yana wahalar da hantar shi ne, sannan zai iya haifar mishi da “hepatotoxicity” (mummunar cutarwa ga hanta).

2. A gujewa amfani da kayan kaifi da wasu suka yi amfani da su, misali; Allura/sirinji, reza da sauransu. Akwai ciwon kumburin hanta (hepatitis), yafi kowanne sauƙin samu.

3. Ayi riga-kafi na ciwon kumburin hanta (hepatitis vaccine), yin hakan zai bada kariya na akalla shekaru 20 ko fiye da haka. Domin mutane da yawa suna ɗauke da shi ciwon kumburin hanta ba tare da sun sani ba kuma wasu na ɗauka daga jikin su.

4. A gujewa Shaye-Shaye, tun daga giya (giya/barasa tafi komai illata hanta) har su shisha, maganin tari (wanda wasu ke Shaye-Shaye da su).

5. A lura da yanayin nauyin jiki/ƙiba; domin ƙiba da yawa na haifar da cutar kitse na hanta (fatty liver disease).

6. A gujewa yawan cin abincin da ba dafa shi aka yi ba (kayan gwangwani da na zaƙi). A dinga cin abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki, kayan lambu/’ya’yan itatuwa.

7. A gujewa mu’amala na kusanci wanda ba aure tsakani (jima’i, sunbata da rungume rungume). Yin jima’i da mai ɗauke da ciwon kumburin hanta na iya sa mutum ya kamu dashi, kun ga yi da wacce ko wanda ke da abokan mu’amala da ba aure tsakani na iya ɗauka a saukake. Toh a kiyaye, a tsaya ga halas kaɗai.

8. A dinga kula da tsaftar jiki da muhalli, a yawaita wanke hannu wa da ruwa.

9. A dinga motsa jiki sosai domin inganta lafiyar ita hantar da ma jiki gaba ɗaya.

10. A takaita mu’amala ko shiga inda sinadarai masu cutarwa (toxins and chemicals) suke.

11. A dinga zuwa dubiyar lafiya asibiti lokacin bayan lokaci.A sani cewa lafiyar mutum ya ta’allaka da lafiyar hantar shi. A kiyaye sosai.

Daga Pharmacist Musa A Bello, ɗan Zaria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories