Wasu da ake Zargin ‘Yan Boko Haram ne sun hallaka Manoma 13 a Borno

Akalla manoma 13 ne suka rasa ransu yayin da wasu da dama suka bace a wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kaiwa manoman shinkafa a gonakinsu da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno da yammacin Lahadi.

 An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun afkawa gonakin shinkafa inda suka damke manoman da suke girbin amfanin gonakinsu a yankin Karkut da Koshebe a karamar hukumar Mafa, inda suka yanka su da wukake.

”Muna cikin bakin ciki game da faruwar lamarin . Hukumomin tsaro da CJTF na ci gaba da neman wadanda suka bata amma kawo yanzu an yi nasarar gano gawarwaki 13,” inji wata majiya.

 Wata majiya mai karfi ta jami’an tsaro ta ce ‘yan ta’addan sun zo akan babura inda suka kasu zuwa rukuni uku sannan su ka far wa manoman.

 Majiyar ta ce maharan sun yi amfani da wukake ne a maimakon bindigogi .

 “An gano gawarwaki tara a jiya lahadi, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bazama ba a san inda suka nufa ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories