Yadda Wani Yaron Kamfani Ya aikata abin Allah wadai Ga Ɗan Ubangidan Sa

Rundunar ƴan Sandan jihar Gombe ta Chafke wasu mutun huɗu bisa zargin su da laifin sace tare da kashe Al’amin Ahmadu ɗan kimanin shekaru 16 da haihuwa.

 Wadanda ake zargin sun hada da Ahmadu Ibrahim mai shekaru 25 da kuma Babuka Abubakar mai shekaru 35.

 Sauran sun hada da Abdulsalam Mohammed mai shekaru 28 da Muhammadu Abubakar mai shekaru 28,dukkansu sun fito ne daga unguwar Liji da ke karamar hukumar Yalmatu Deba a jihar Gombe.

 

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a yau juma’a, jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mahid Abubakar, ya ce rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta samu ƙorafi daga wurin wani Ahmadu Yaya,wato mahaifin marigayi wanda yake zaune a Arawa quarters, inda ya basu rahoton cewa wasu da bai san ko su waye ba ne sun kira shi inda suka sanar mishi da shi cewa sun yi garkuwa da Ɗansa sannan suka bukaci Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa.

A cewar Abubakar, Yaya ya kuma bayyana cewa dansa Alamin dalibin Ubaida Academy Arawa ne wanda ya bar gida domin yin wata sana’a, inda ya kara da cewa bai dawo ba har sai da aka yi masa waya yana neman a biya shi Naira miliyan biyar.

 Ya ci gaba da cewa, “Da samun wannan ƙorafin, sashin yaki da garkuwa da mutane karkashin kungiyar O/C Anti Kidnapping ya dauki matakin kama wadanda ake zargin kuma nan take suka fara bincike.  A Wani bincike da aka yi ya nuna cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Ahmadu Ibrahim, ya kasance yana aiki a kamfanin sarrafa shinkafa na mahaifin shi yaron .

 “Wanda ake zargin nan take ya amsa laifin yin garkuwa da Al’amin , kuma sun kaishi dutsen Lijji amma daga baya sai suka shi sakamakon mahaifinsa ya kasa biya kudin fansa naira 700,000 kamar yadda aka amince a baya ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho, wadanda ake zargin a yanzu haka suna hannun ƴan sanda kuma za a gabatar da su a gaban kotu domin a gurfanar da su gaban kuliya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories