Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama a Ƙauyukan Zamfara

Wasu ƴan bindiga sun sace mutane 150 wanda yawancinsu mata ne da yara a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a jiya Juma’a.

 Hakazalika ƴan bindiga sun kashe mutum ɗaya a harin da suka kai wanda ya dauki tsawon sa’o’i ana yi, kamar yadda wani mazaunin garin ya bayyana.

 Wannan hari ya faru ne mako guda da sace mutane 17 a ƙauyen Ruwan Ɗorawa da ke karamar hukumar.

 Jaridar Daily Trust ta gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmakin ne a kauyuka huɗu da suka haɗa da Mutunji, Kwanar-Dutse, Sabon-Garin Mahuta da Unguwar Kawo a farmakin da aka kai na baya-bayan nan.

Wani mazaunin ɗaya daga cikin kauyukan da aka kai hari garin mutunji ya ce ƴan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a, sun kai farmakin ƙauyuka hudun ne duka a lokaci ɗaya.

 Ya ce: “Nan take suka shiga kauyen Mutunji, tare da fara harbe-harbe a iska don tsorata mazauna garin.  Kamar yadda ake tsammani, mutane sun fara gudu don tsira da rayukansu.

“Daga nan ne ‘yan bindigar suka yi nasarar kame masu raunin cikin ƴan kauyen waɗanda galibinsu mata da yara ne.  Masu jini a jika sune suka yi nasarar tserewa. A lokacin da suke kai harin na yi ƙokarin kiran wani abokina da ke ƙauyen Kwanar-Dutse da ke makwabtaka da mu domin neman taimako amma sai ya shaida min cewa su ma ana kai musu harin ne a Wannan lokaci.

 Ƴan Bindiga sun yi nasarar kurdawa da waɗanda suka sace cikin daji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories