Mazauna Tudun Biri Sun Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu

Mazauna ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun maka gwamnatin tarayya a kotu inda suka buƙaci da a biya su diyyar Naira biliyan 33 kan harin da sojojin sama suka kai wanda ya yi sanadiyyar rayuka sama da mutane 100.

 Lamarin dai ya faru ne a daren ranar Lahadin yayin gudanar da bikin Maulidi. 

Bayan faruwar lamarin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan faruwar lamarin tare da bada tabbacin hakan ba zata sake faruwa ba.

 Mazauna garin sun shigar da ƙarar ne a ranar 8 ga watan Disamba a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta hannun Alhaji Dalhatu Salihu a madadin mutanen ƙauyen da taimakon lauyansu, Mukhtar Usman Esq.

 Sannan kuma sun nemi da a buga lamarin a gidajen jaridu aƙalla guda uku .

 Sun ce an shigar da karar ne domin a tabbatar da an karbi haƙƙin wadanda suka tsira da rayukansu a faruwar lamarin.

 Daga cikin haƙƙokin da suke nema akwai kashe mutane,da aka yi ta hanyar tashin bama-bamai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama wanda hakan  ya yi daidai da take haƙƙin kisa sashe na 33 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, 1999 da sashi  10 ya tanada.  (1) na Dokar Yarjejeniya ta Afirka kan Hakkokin Dan Adam da Jama’a (Ratification Enforcement) Act (Cap 10) LFN 2010 .

Har yanzu ba a tsayar da ranar da za a saurare zaman shari’ar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories