Ma’aikatan Lafiya A Borno Zasu Sami Ƙarin Albashi Da Kashi 30

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi wa ma’aikatan lafiya da suka amince za su yi aiki a ƙauyuka alƙawarin karin kashi 30 na albashi.

 Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin raba Naira 100,000 da kayan abinci ga tsofaffi – masu shekaru 65 zuwa sama ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative wanda Uwargidan Shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta ƙaddamar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa a shirye take don ta tallafa wa tsofaffi ta kowace hanya, Ya kuma ƙara da cewa jihar a shirye take don ta samar da likitocin da suka ƙware wajen kula da tsofaffi a cibiyoyin lafiya a fadin jihar.

 Zulum, wanda ya samu wakilcin Farfesa Baba Malam Gana, kwamishinan lafiya na jihar, ya bayyana cewa za a kuma kafa sashen kula da tsofaffi a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Borno da ke garin Maiduguri.

Da take ƙaddamar da rabon Naira 100,000 ga tsofaffi, uwargidan gwamnan jihar  Dakta Falmata Zulum, wacce ta wakilci Uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu, ta ce tsofaffi 250 ne suka ci gajiyar tallafin.

 Uwargidan Ta ce an an ƙaddamar da wannan shiri ne don rage raɗaɗin halin da ake ciki .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories