Wani Basarake a Najeriya ya ɗaura aniyar zama wanda ya fi kowa daɗewa yana kallon TV a Duniya

Wani Basarake a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya ya kama hanyar shiga Kundin Bajinta na Guiness wato Guinness World Records da nufin zama mutumin da ya fi kowa dadewa yana kallon Talabishin a Duniya.

Basaraken mai suna Sanya Atofarati, ya zauna yana kallon Talabishin kimanin kwanaki biyar wanda hakan ne ya ɗauke shi awanni 120.

Ya fara kallon Talabishin din ne tun daga ranar Laraba 27 ga watan Disambar shekarar bara har zuwa ranar 1 ga watan Janairun shekarar da mu ke ciki.

Hakan dai zai baiwa Sanya Atofarati damar ƙalubalantar Fragoso ɗan asalin ƙasar Amurka da ya shiga Kundin Bajintar a matsayin wanda ya fi kowa dadewa yana kallon Talabishin a Duniya.

Fragoso dai yana riƙe da kambun ne tun daga shekarar 2016, bayan da ya shafe awanni 94 yana kallon Talabishin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories