Shugaban Ƙaramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ya Shaƙi Iskar Ƴanci

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sakin shigaban karamar hukumar Akwanga, Safiyanu Isah Andaha wanda aka sace tare da wasu mutane uku.

Kakakin rundunar, Ramhan Nansel ya tabbatarwa da manema labarai cewa jami’an tsaro sun kubutar da Safiyanu Isah Andaha.

A daren ranar Laraba ne ‘yan fashin dajin suka saki shugaban karamar hukumar da sauran mutane ukun da suka sace, ko da ya ke wasu rahotanni na cewa sai da aka biya kudin fansa.

Sai dai jami’in’yan sandan ya musanta haka.

Ya kuma kara da cewa an kai mutanen hudun babban asibitin gwamnatin tarayya da ke birnin Keffi domin duba lafiyarsu.

A daren ranar Talata ne wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka farwa motocin da ke dauke da shugaban karamar hukumar, Safiyanu Isah Andaha, kuma suka yi awon gaba shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories