Hukumar EFCC Ta Damke Shugabannin Bankunan Zenith Da Jaiz Da Providus

Wannan matakin ya zo a dai-dai lokacin da hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa ke gudanar da bincike kan wani shirin satar kudaden gwamnati da ke da alaka da tsofaffin ministocin harkokin jin kai ta da, da ta yanzu -Betta Edu da Sadiya Umar Farouq.

Shugabannin da abin ya shafa sun hada da Dr. Ebenezer Onyeagwu na Bankin Zenith da Haruna Musa na Bankin Jaiz, da Walter Akpani na Bankin Providus.

Majiyoyi masu inganci wadanda suka tabbatar da wannan ci gaban bisa sharadin boye sunansu, sun ce an kama mutanen ne a ranar Talata.

A cewar majiyar, shugabannin bankunan da aka dade ana zarginsu da taimakawa wajen karkatar da kudaden jama’a zuwa wasu asusun sirri, yanzu haka suna hannun EFCC.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta bankado wasu makudan kudade da aka bankado a asusun gwamnati, wadanda Edu da Farouq suka amince da su a matsayin minista.

Sadiya Umar-Farouq wadda ta jagoranci ma’aikatar jin kai a gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari, ana kuma zarginta da karkatar da naira biliyan 37 da aka ware domin shirin mika kudaden da aka kayyade a lokacin mulkin shugaba Buhari.

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale bai samu damar tabbatar da faruwar lamarin ba ya zuwa lokacin da aka buga labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories