Ban yi Wata Yarjejeniya Da Tinubu Akan Hukuncin Kotun Ƙoli Ba – Kwankwaso 

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaben da ya gabata, ya ce shi bai yi wata yarjejeniya da shugaba Bola Tinubu ba, ko kuma wani mutum dangane da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke a zaɓen Kano ba.

 Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin cewa ya cimma yarjejeniya da Tinubu kafin yanke hukunci.

Da yake zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce, “Abin da ya faru a kotun ƙoli babban darasi ne a gare mu baki ɗaya. Ni ban ƙullaci kowa a rai ba. Tsawon lokacin, ban yi wa kowa komai ba.  Kuma kowa zai girbi abin da ya shuka. Ni dai iyakar sanina ban cimma matsaya da kowa ba.

Kwankwaso ya kuma ƙara da cewa ba zai yi katsalandan game da gudanar da mulkin Kano ba shi dai kawai zai zamo mai ba da shawara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories