Matashi Ya Datse Hannun Budurwa Saboda Ta Ƙi Amincewa Soyayyarsa

A ranar 6 ga Janairu, 2024 a ƙauyen Kagbé, da ke cikin Ngalo Canton na lardin Barh Sara, wani saurayi ya datse hannun wata yarinya da ake zargin ta ƙi ci amince wa tayin soyayyarsa.

Yarinyar ta faɗa cikin matsanancin baƙin ciki a sanadin rasa hannunta na hagu.

Wani matashi mai neman aurenta da ake kira Djounoutangué, mazaunin ƙauyen Bédang na ƙasar Chadi, wanda ke maƙwabtaka da ƙauyen da yarinyar ta ke, shi ne ya aikata wannan ɗanyen aikin.

Bisa ga rahoton da jaridar Têcor Média ta ruwaito, abin takaicin ya auku ne lokacin da Djounoutangué ya yi shelar soyayya ga yarinyar, wacce ta ba shi abin da ya ɗauka mummunar amsa.

Rashin gamsuwa da wannan ƙiyayyar ya sa Djounoutangué ya yanke shawarar ɗaukar matakai mai tsauri kan budurwar.

Don haka sai ya shirya yi wa yarinyar kwanton ɓauna, kuma ya kai mata hari yayin da ta dawo daga ziyarar iyayenta.

Matashin na ɗauke da adda, kuma nan take ya kai wa yarinyar hari da makamin.

Ko da yake ta yi nasarar kare harin da farko, amma saran da ya riƙa kai mata da adda ya kai ga samun hannunta na hagu.

An yi gaggawar kai ta zuwa asibitin Moïssala, inda likitoci suka lura cewa ƙaramar fata ce kawai ke riƙe hannun. Yankewar hannun ne shi ne kawai zaɓi domin ceton rayuwar wannan budrwar da aka azabtar.

Har ya zuwa yanzu, Djounoutangué ya kasance ba a iya gano inda ya shiga ba, duk da haɗin gwiwa na jandarmomi na Béboro da Moïssala.

Wannan bala’in na Kagbé ya nuna gaggawar ƙara wayar da kan jama’a game da cin zarafi da suka danganci jinsi, yayin da ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin hukunta waɗanda ke ci gaba da yin irin wannan munanan ayyuka a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories