Na Rungumi Ƙaddara-Cewar Nasir Gawuna

Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Kano, ya ce ya karɓi hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamna a jihar a matsayin abinda Allah ya hukunta.

 In ba a Manta ba Dai A jiya Juma’a ne Kotun Koli ta tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matmatsayin Halastaccen gwamnan Jihar Kano.

Gawuna Ya ce: “Wannan hukunci hukuncin Allah ne kuma mun yarda da shi.  Kamar yadda muka yi addu’a cewa idan ya dace a gare mu ya ba mu daga falalarSa, idan kuwa ba haka ba ne ya musanya shi da mafi alheri. 

Muna da yakinin cewa Ubangiji ya amsa addu’o’inmu.  Shi ne Mai hikima.  Muna godiya ga Allah maɗaukakin sarki.

 “Magoya bayanmu su fahimci cewa Allah Madaukakin Sarki shi ne ya tsara komai kuma ya ƙaddara faruwar hakan. Kowa ya yi haƙuri ya yarda da hukuncin Allah.

“Sakona ga al’ummar Jihar Kano shi ne a zauna lafiya kuma a yi biyayya ga shari’a.  Su yi biyayya.  Jama’a su cigaba da addu’a.  Allah ba ya kuskure.  Shi ne Masani.  Mu ci gaba da addu’ar zaman lafiya a Jihar Kano da ma Nijeriya baki daya;  kuma muna rokon Allah ya azurta mu da arziki da lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories