Mako Na Guda Ban Yi Bacci Ba,Ina Yaƙin Ƙwato Kujera ta – Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana yadda ya shafe kwanaki bakwai bai yi barci ba a garin Abuja ,yana fafutukar hana tsofaffin ƙusoshin jihar Bauchi ƙwace nasararsa a zaɓen da ya gudana.

 Gwamnan a jawabin sa ya kuma yabawa shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan rashin sauraron su,inda suka ƙyanƙyasawa  shugaban ƙasar cewa shi barazana ce gareshi.

 Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a gidan gwamnati da ke Bauchi a yayin gudanar da wani gangami da aka shirya masa, inda ya kuma ce an ba shi damar bin doka da oda.

 “Ya ku Mutanen Bauchi tabbas kun nuna min halaccin da kuma soyayya, kun ba ni amana kuma ba zan yi ƙasa a gwiwa ba saboda kwana na bakwai ban yi barci ba don kawai in tabbatar da ann dawo mana da wannan kujera.  Wasu sun haɗa kai – tsofaffin ƙusoshin jihar Bauchi aka je aka shirya min ƙarya cewar Ni zan kasance matsala ga shugaban ƙasa amma kuma hakan bai samu ba.

 “Ina godiya ga ɓangaren shari’a na Najeriya musamman kotun ƙoli, ina godiya ga gwamnatin shugaba Tinubu da ta yi imani da shugabanci na gari wanda ya ba da damar bin doka da oda ba tare da la’akari da ƙarairayi da munanan sharrida aka yi.  Mi ni ba. Ina godiya ga Mataimakin Shugaban ƙasa da dukkan abokan aikinmu a matakin tarayya.  Ba wani abinds zai girgiza mu,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories