Majalisar Shari’ar Musulunci Ta Buƙaci Tinubu Ya Kori Ministoci Marasa Gaskiya

Majalisar ƙoli ta shari’a musulunci a Najeriya (SCSN), ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya chanza gurbin ministocin da ba su da gaskiya wajen yi wa kasa hidima.

 Kungiyar ta koka ne duba da irin taɓarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ta shiga tun bayan hawan Tinubu kan karagar mulki, ta kuma ce tikitin ‘Muslim-Muslim’ da shugaban kasar ya dauka wajen yin nasara a zaben da ya gabata bai kawo wa al’ummar Musulmi wani cigaba ba.

Shugaban majalisar, AbdurRasheed Hadiyyatullah, wanda ya bayyana haka a wajen taron ƙasa da aka gudanar ranar Talata a Abuja, ya ce duk da dimbin goyon bayan da shugaban ya samu, ‘yan Najeriya ba su ci moriyar dimokradiyya ba tun bayan hawansa karagar mulki.

 Shugaban ya ce dalilin da ya sa ƴan Najeriya da dama ke goyon bayan tikitin ‘muslim-muslim’shi ne don ganin yadda za a samar da ci gaba ga kasar nan, inda ta ce babu abin da aka cimma a cikin watanni bakwai da hawa mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories