Kano:Kotu Ta Aike Da Wani Jigon Jam’iyyar APC Gidan Yari

An kama wani babban ɗan’adawa a Kano Danbilki Kwamanda tare da tasa keyarsa zuwa gidan yari.

Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda bisa zargin yin wasu maganganu da ake zargin za su iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano.

Hukumar DSS ce ta fara gayyatarsa tare da miƙa ga shi ƴan sanda, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa BBC.

“Ana zarginsa da yin wasu kalamai na tunzura jama’a kan batun masarautu a jihar Kano,” in ji shi.

Sai dai ya musanta zargin da ake ma sa a kotun.

Ya yi kalaman ne a wani gidan rediyo a Kano, bayan kalaman jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun makomar masarautu a jihar ta Kano.

A cikin kalamansa da suka janyo kama shi, Danbilki ya ce ba za su yarda da cire sarakunan ba.

Kotu ta bayar da umarnin tafiya da shi gidan gyara hali na Goron Dutsi a Kano.

Sai a ranar 29 ga watan Janairu kotu za ta saurari bukatar belinsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories