Shugaba Tinubu Ya Nemi Kwankwaso Da Ganduje Su Sasanta

Shugaba Bola Tinubu ya fara yunƙurin sasanta jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso da kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

 Wasu majiyoyi da dama sun tabbatar wa Daily Trust cewa a ranar Litinin da ta gabata shugaban ya bayyana aniyarsa ga shugabannin biyu a zantawa mabanbanta kuma ya ba su lokaci domin su sanar da masu ruwa da tsaki manufarsa, domin tsaida matsaya game da sasantawar su .

A ranar Alhamis shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da wasu zaɓaɓɓun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga jihar Kano, sannan kuma ya sami ganawa da Kwankwaso a ranar Lahadin da ta gabata, a ƙoƙarin sa na shirin sasan tasu inda ake sa ran kowanne daga cikin su zai zo da mutum biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories