Matar El-Rufa’i Ta Yi Barazanar Hukunta Matan Arewacin Najeriya Kan Munafurci

Sirikar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i wato A’isha Habibu ta yi barazanar hukunta matan Arewacin Najeriya saboda yadda suke yada gulmace-gulmace a shafukan sada zumuta bayan wata ta tsokane ta a shafin Instagram kamar Rfi Hausa ta rawaito

Rikicin na shoshiyal midiya ya samo asali ne bayan wata mai suna Zainab ta yi wa A’isha katsalanda a rayuwarta ta aure, tana tambayar ta kan dalilin rashin ganin hotunanta da mijinta, Bello El-Rufa’i a shafukan sada zumunta akai-akai.

Wannan tambayar ce ta harzuka A’isha wadda ta mayar da martanin cewa ” rayuwar aurenta ba ta fallasa ba ce.”

Ashe haka muka lalace a matsayinmu na al’umma? Kullum, ina yin addu’a ga ‘yan uwana ‘yan Arewa don ganin rayuwarsu ta inganta. Kar ku bari gulma da tsegumi su mamaye rayuwarku. Inji A’isha.

Kazalika sirikar ta El-Rufa’i ta kalubalanci Zainab kan cewa, in ta isa, ta zo ta lakace mata hanci gaba da gaba kuma a bainal jama’a da irin wannan kalmar, inda ta ce, a nan za ta gane kurenta.

A cikin shekarar 2023 ne, A’isha ta auri dan tsohon gwamnan Kaduna, kuma ita ‘ya ce ga Kanar Habibu Shu’aibu, tsohon kantoman soja a jihohin Filato da Niger da ke Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories