Bam Ya Hallaka Manoma 11 A Maiduguri

Manoma 11 ne suka mutu a Firgi da ke Unguwar Pulka a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno bayan da suka taka wasu abubuwa masu fashewa.

Wata buɗaɗɗiyar mota da ke jigilar manoman zuwa gonakinsu ta taka wasu bama-bamai waɗanda suka fashe, inda manoman da wasu mutane biyu a kan kekunansu suka mutu nan take.

A cewar wata majiya a bangaren ayyukan jin kai, an dasa bam din ne a kafadar babban titin da ke kan hanyar zuwa gonakin nasu.

Duka fasinjojin motar sun mutu yayin da direban ya samu munanan raunuka wanda ya saka shi cikin mawuyacin hali.

Ba a tabbatar da lokacin fashewar ba amma majiyar ta ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.

Ana zargin ƴan ta’addan Boko Haram ne suka tayar da bam din da suka sake kai hare-hare kan matafiya a cikin al’ummomi a jihar Arewa maso Gabas.

Lamarin na ranar Litinin ya faru ne kwana biyu bayan da wasu ɗalibai shida na Tsangayar karatun Al-kur’ani da ke garin Gubio suka mutu a wani harin bam da ya tashi a kusa da tsangayar a ƙaramar Hukumar Gubio ta Jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories