Masu sana’ar Gurasa na zanga-zangar lumana kan tsadar Fulawa a Kano

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa masu sayar da Gurasa na zanga-zangar lumana kan tsadar Filawa.

Gidan Rediyon Freedom ya wallafa hotunan matan da ke zanga-zangar lumanar dauke kwalaye masu rubutun da ke bayyana halin da su ke fuskanta.

Zanga-zangar lumanar na zuwa ne a daidai lokacin da buhun fulawa ya tashi daga N35,500 yanzu ya koma N44,000.

Tashin kayan masarufi ya munana a Najeriya cikin kwanakin nan.

Lamarin ya ƙazance ne sanadiyyar wasu daga cikin shirye-shiryen da gwamnati ta ɓullo da su, kamar na cire tallafin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories