Masu Raunin Zuciya Su Guji Kallon Wasan AFCON,Likita Ya Gargaɗi Ƴan Najeriya

Wani Likita da ke garin Akure kuma Babban Darakta na Asibitin Sckye, Dokta Thomas-Wilson Ikubese, ya gargaɗi magoya bayan Super Eagles masu rauni a zuciya da su gujewa kallon wasan da za a buga rana Lahadi.

 Mista Ikubese, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka bayyanawa manema labarai a yau Juma’a a garin Akure, Inda ya ke cewa duk wanda ya san yanada rauni to ya kiyaye abinda zai je ya dawo.

 Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya labarto cewa, Super Eagles za ta kara da mai masaukin baki, ƙasar Cote D’ivoire, a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON.

In ba a Manta ba kimanin ƴan Najeriya huɗu ne suka rasa ransu a sakamakon bugun zuciya yayin kallon wasa da ya gudana tsakanin Ƙasar Afirka ta Kudu Da Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories