Ƴan Sanda Sun Musunta Iƙirarin Jami’an NSCDC Kan Shigar Ƴan Bindiga Jihar Gombe

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta yi watsi da ikrarin rundunar tsaron NSCDC dake aiki a jihar, cewar ‘yan binda sun kutsa kai wasu yankunan jihar domin kai hare hare.

Kakakin rundunar ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya ce babu wata barazanar da mazauna jihar Gombe ke fuskanta a halin yanzu, saboda bayanan asirin da suke da shi sun nuna cewar jihar na cikin kwanciyar hankali.

Abubakar yace babu gaskiya cikin bayanan shugaban hukumar NSCDC dake jihar, Muhammad Bello Mu’azu wanda ake ta yayatawa, inda yake bayyana kutsa kai da ‘yan bindigar suka yi zuwa cikin jihar.

Sanarwar kakakin ‘Yan sanda tace suna tabbatarwa jama’ar jihar Gombe cewar babu wata barazanar da suke fuskanta a halin yanzu, yayin da suke hada kai da sauran hukumomin tsaron dake aiki a jihar dan tabbatar da tsaron al’umma.

Kakakin ‘Yan sanda ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba, yayin da roke su da su shaidawa jami’an su duk wani mutum ko wata kungiyar da aka gani ta na neman tada hankali.

Wannan martani ya biyo bayan gargadin da shugaban hukumar NSCDC na jihar, Muhammad Bello Mu’azu ya gabatar ne a ranar talatar da ta gabata, wadda ke cewa ‘yan bindiga na kwarara zuwa jihar.

Masana na kallon wannan martani a matsayin gibin da ake samu wajen rashin aikin yi tare a tsakanin hukumomin tsaron dake jihar.

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin dake zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories