AFCON: Kashim Ya Ɗage Zuwa Ƙallon Wasan Ƙarshe A Ivory Coast 

Mataimakin shugaban Ƙasa Kashim Shettima a yau ya ɗage zuwa ƙasar Ivory Coast domin kallon yadda za ta kaya a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).

In ba a Manta ba a wata sanarwa da ta fito a ranar juma’a anji Shugaban CAF yana cewa shugaba Tinubu zai halarci wasan ƙarshe da za a yi.Amma sai dai da alama haka ba za ta samu ba domin Kashim ya ɗage zuwa kallon wasan ya wakilci shugaban Tinubu.

Haka ma Wasan da aka buga tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya a gaban idon sa aka yi a Stade de la Paix a Bouake inda Super Eagles ta yi nasarar doke a Afirka ta Kudu da ci 4-2 a bugun fenareti.

Najeriya dai za ta kara ne da mai masaukin baƙi a wasan ƙarshe da za a yi a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, babban birnin ƙasar Cote D’Ivoire, ranar Lahadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories