Har Yanzu Bamu Sayar Da Kujerun Hajji Sama Da Dubu 3 Ba – Hukumar Alhazan Kano

Hukumar kula da ayyukan haji ta jihar Kano dake Najeriya ta sanar da cewar daga cikin kujeru dubu 5 da 934 da hukumar ta kasa ta ware wa jihar, ya zuwa wannan lokaci kujeru dubu 2 da 600 kawai aka sayar, yayin da har yanzu kujeru sama da dubu 3 na can ba a sayar ba.

Shugaban hukumar Alhaji Laminu Rabiu ya gabatar da wadannan alkaluma a lokacin da yake bude taron bitar horar da maniyata aikin hajin bana daga jihar wanda aka saba gudanarwa kowacce shekara.

Laminu bai bayyana dalilan da suka haifar da jinkirin sayar da kujerun ba, lura da cewar lokacin fara aikin hajin na kara karatowa, amma masu sa ido na danganta matsalar da tsadar kujerar da ake fuskanta bana saboda faduwar darajar naira.

Ya zuwa wannan lokaci ana sayar da dalar Amurka guda a kan kusan naira 140, yayin da aikin hajin ana masa lisasfi ne da kudin dala wanda za’a biya kamfanonin jiragen sama da zasu kai maniyata da kuma daukar gidajen hayar da ake aje maniyata a kasar Saudi Arabia.

Hukumar alhazai ta Najeriya tace maniyatan bana daga yankin arewacin kasar za su biya naira miliyan 4 da dubu 699, yayin da wadanda suka fito daga kudancin Najeriya kuma zasu biya naira miliyan 4 da dubu 899, sai kuma maniyatan Yola da Maiduguri da za su biya naira miliyan 4 da dubu 679.

A kowacce shekara jihar Kano ce ke sahun gaba wajen gabatar da maniyata aikin hajjin da suka fi na kowacce jiha yawa a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories