Tsadar Rayuwa: Gwamna Zulum Ya Buƙaci A yi Azumi Da Addu’o’i Na Kwana Ɗaya

Gwamna Babagana Zulum ya bukaci al’ummar jihar Borno da su ɗau niyyar Azumi tare da gudanar da addu’o’i na musamman a ranar litinin kamar yadda aka saba yi a baya don neman taimakon Allah kan halin ƙunci da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta.

 A jawabinsa gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar, sarakunan gargajiya, malamai da ma sauran ƴan ƙasa da su yi azumin kwana ɗaya a ranar Litinin domin neman zaman lafiya da ci gaban jihar.

 “Na damu matuƙa da irin wahalar tsadar rayuwa da ƴan ƙasa ke fuskanta a ƴan kwanakin nan, musamman ma tsadar kayan abinci.

“N san irin matsayin da ake ciki, kuma ina so in tabbatar muku da cewa mun dauki ƙwararan matakai don magance matsalar.

 Gwamnatinmu za ta maida hankali wajen farfado da harkar noma, don ƙara samar da abinci don rage dogaro da abincin tallafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories