Tsadar Rayuwa:Jihar Borno Ta Fara Shirin Sauƙaƙawa Ƴan Kasuwa Haraji

Hukumar tara haraji ta jihar Borno (BOIRS) ta ce ta ɓullo da shirin rage haraji domin rage wahalhalu da kuma sauƙin kasuwanci a jihar.

 Shugaban hukumar Farfesa Bello Alhaji Ibrahim shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Maiduguri ranar Asabar.

Ibrahim ya bayyana cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanya hannu a kan dokar zartarwa don magance ƙorafe-ƙorafe.

 Ya kuma yi nuni da cewa, duk gwamnatoci sun dogara ne akan kuɗaden haraji domin gudanar da ayyukan raya kasa masu muhimmanci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories