Da Ɗumi-Ɗumi-Ƴan Bindiga Sun Dira Wata Makaranta,Sun Yi Awon Gaba Da Ɗalibai A Kaduna

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai firamare da na sakandare kusan su 200 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau Alhamis lokacin da ɗalibai ke taron Asambili da misalin karfe takwas da rabi na safe.

 Wani babban jami’i a jihar Kaduna ya tabbatar wa da BBC Faruwar lamarin sai dai ya ce ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories