Rafael Nadal ya fice daga gasar Indian Wells sa’o’i 24 kafin wasansa na zagayen farko da Milos Raonic

Rafael Nadal ya fice daga gasar Indian Wells sa’o’i 24 kafin wasansa na zagaye farko da Milos Raonic ranar Juma’a.

Nadal, mai shekaru 37, ya koma Brisbane International da aka dade ana jira, bayan shafe kusan shekara guda yana jinya.

Sai dai dan wasan na Spaniya ya samu rauni a kugunsa a gasar, wanda ya hana shi shiga gasar Australian Open.

Nadal ya buga wasa da Carlos Alcaraz a ranar Lahadi, amma ya ce har yanzu bai shirya taka leda a matakin koli ba.

A watan Mayu, bayan tilasta masa barin gasar French Open a karon farko cikin shekaru 19, Nadal ya ce 2024 “watakila” ita ce shekarar karshe ta wasansa.

A watan da ya gabata, tsohon dan wasan na daya a duniya ya ce bai da tabbacin ko gasa nawa zai iya shiga kafin ya yi ritaya, amma ya kara da cewa “ba ya tunanin zai yi wasa da yawa.

Gasar Nadal ta gaba mai yiwuwa ta kasance a gasar da ya fi so a Monte Carlo Masters na wata mai zuwa, inda ya zama zakara har sau 11.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories