African Games: Falconets ta fara wasa da kafar dama a gasar wasannin Afrika

Falconets ta Najeriya ta fara wasa da kafar dama a gasar wasannin Afrika da ke gudana a birnin Accra na kasar Ghana yayin da suka samu maki a wasansu na farko na rukuni.

‘Yan wasan Najeriya sun fara karawa ne da Morocco a yammacin Juma’a kuma sun samu nasara da ci 2-0 akan tawagar Cape Coast. Fatima Bambara ta ci gida, wanda ya fara ba Najeriya damar shiga gaba a wasan.

Falconets dai ta kara shiga gaba ana daf da tafiya hutun rabin lokaci inda Yina Adoo ta zura kwallo ta biyu a minti na 40 da fara wasa.

Kasar da ke arewacin Afirka ta fi taka rawar gani a zagaye na biyu na wasan amma sai dai sun kasa fasa bayan Falconets a wasan da aka tashi 2-0.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories